Daga Nura Abubakar
Shugaban karamar hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban kauye farawa ya Bayyana Damuwa gami da kaduwa da samu labarin Rasuwar Daliban kusan 5, Yan makarantar kwalajin ilimi ta sa’adatu Rimi, sakamakon Hadarin mota akan haryar Kano zuwa katsina.
Cikin Wata sanarwa da Mataimaki na mis Kan harkokin yada labarai ga Shugaban Karamar Hukumar Shazali Saleh farawa ya aikowa Kadaura24 yace Shugaban karamar hukumar ta Kumbotso Cikin Alhini ya Aike da sakon Ta’aziyya ga Mai Girma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, kwamishiniyar ilimi Mai zurfi Dr mariya Bunkure da shugaban Kwalajin Dr yahaya Isa Bunkure da Kuma Daliban makarantar, sai iyayen Daliban Yan Uwa da abokan arziki sai Kuma Al’ummar jihar Kano musamman na karamar hukumar Kumbotso.
Cikin wani sako Ta’aziyya Daya wallafa Dauke dasa Hannun maitaimaka Masa na musamman Kan harkokin yada labarai Shazali Farawa, alhaji Hassan yace.
“Innalillahi wa inna illaihir Raji’un, Ina Adu’ar Allah ya jikansu, yakai Rahama kabarinsu ya Kuma baiwa marasa lafiyan cikinsu koshin lafiya”
Akarshe yace Allah Daya karbesu yafimu son su, Yana Kuma Amfani da wannan Dama wajen Mika sakon Ta’aziyyar ga kungoyoyin Dalibai bisa wannan Baban Rashi.