Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Abdulkadir Gaya ya karbi takardar nadinsa na zama sabon Sarkin Gaya mai daraja ta biyu.
Sarkin dai shi ne daya tilo a cikin sarakuna biyar da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi.
Hakan ya biyo bayan amincewarsa ga sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta yi, wadda ta amince da kafa sarakunan Gaya, Rano, da Karaye guda uku masu daraja ta biyu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ta ce an dawo da Aliyu Ibrahim bisa cancanta da kuma jajircewarsa na yi wa al’ummar Masarautar Gaya hidima da suka hada da kananan hukumomin Gaya, Ajingi, da Albasu.
Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya ayyana mafi ƙarancin albashi
“Za ku iya tunawa cewa Sarkin Gaya ne kadai ya karbi kaddara a lokacin da aka rushe masarautu biyar, aka sauke dukkan sarakunan.” Sanarwar ta kara da cewa.
Sarkin Gaya ya isa gidan gwamnatin Kano tare da rakiyar daukacin sarakuna da sauran masu rike da sarautar gargajiya na masarautar.