Daga Sani Idris Maiwaya
A ranar Alhamis nan ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon takin zamani na sama da Naira biliyan daya ga kananan manoma da suka hada da mata da masu bukata ta musamman a jihar.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa kadaura24, ya ce shirin wani mataki ne na cika alkawarin da gwamna Yusuf ya dauka a yakin neman zabe na inganta rayuwa ta hanyar saka hannun jari a harkar noma.
Idan za a iya tunawa kadaura24 rawaito Gwamna Yusuf a lokacin yakin neman zabensa na zaben 2023 ya yi alkawalin kawo sauyi a harkar noma ta hanyar samar da ingantattun kayan aikin noma masu araha kamar yadda yake kunshe a cikin kundin manufofinsa dakeshafi na 70 da ya gabatar wa mutanen Kano mai taken “Alkawarina ga Kanawa.”
Dawakin-Tofa ya bayyana cewa takin zamani samfurin NPK na sama da Naira biliyan daya aka rabawa kananan manoma 52,800 a fadin kananan hukumomi 44 , wanda kamfanin samar da kayan noma na jihar Kano (KASCO) ya samar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a lokacin da yake kaddamar da rabon takin ya bayyana cewa an dau wannan mataki ne da nufin rage tsadar kayan noma da kuma bunkasa samar da abinci a jihar kano.
Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya ayyana mafi ƙarancin albashi
Majalisar zartaswar jihar ta kuma amince da sayo takin zamani na sama da Naira biliyan biyar wanda nan ba da dadewa ba za a samar wa manoman Kano shi a farashi mai sauki.
Ya jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da samar da abinci ta hanyar samar da taki a kai a kai da kamfanin KASCO mallakar jihar zai rika yi. Gwamna Yusuf ya ce ana inganta kamfanin KASCO da sauran cibiyoyin masana’antu na jihar don dawo da kudaden shiga da kuma dorewar tattalin arzikin jihar.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka hada da mata manoma da nakasassu ana sa ran za su samu kilogiram 25 na takin NPK don tallafawa ayyukan noma da kuma bunkasa noma don inganta rayuwar al’umma.