Halin yunwa da ake ciki a Nigeria abun tsoro ne – Atiku Abubakar

Date:

Daga Samira Ahmad

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar hamayya a shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa halin yunwa da ake ciki a kasar nan manufofin gwamnatin APC karkashin jagorancin Tinubu ne su ka haifar da shi babu gaira babu dalili.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce rashin samar da matsaya kan mafi karancin albashi da zai yi dai-dai da yanayin rayuwar da ake ciki, zai zama mummunar barazana ga rayuwar ma’aikata da iyalen su a matakan gwamnatocin tarayya, jiha da kananan hukumomin kasar nan.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka aikowa kadaura24.

Karin Haske Kan Hukuncin Kotu Game da Rikicin Masarautun Kano

“Tun bayan da gwamnatin Tinunbu ta janye tallafin man fetur bagatatan ba tare da kwakwaran nazari ko tanadi ba, da karya darajar Naira wanda shi ma ba tare da lakari da siffofin tattalin arzikin kasar da ya dogara kachokan a kan shigo da abubuwan masarufi sarrafafu ko wanda za a sarrafa ba, rayuwar yan kasa ya shiga ma wuyacin hali”. A cewar Atiku Abubakar

Talla

A yanzu shugaba Tinunbu na shirin ciwo bashin dala biliyan 2 kari akan dala kusan biliyan 3 da rabi, wanda ba a san manufar cin bashin ba, inda zargi yai kwari cewar bashin na tabbatar da walwalar fadar gwamnatin tarayya ne da manyan jami’an gwamnatin.

Jagoran yan hamayyar na Nigeria ya ce Wannan mummunan bashin zai kara yawan bashin da ake bin kasar zuwa kusan kimanin dalar amuruka billiyan 100 wannan zai kara ma gembo gishiri wajen ta’azzara mummunan halin da jama’a ke ciki. Wannan ba karamin bakin labari ba ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...