Daga Halima M Abubakar
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya shawarci cewa sanya dokar ta baci ba zai magance kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta ba.
Masari ya ba da shawarar ne a ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyin manema labaran fadar gwamnati bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Idan za a iya tunawa, majalisar wakilai a ranar Talata ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta sanya dokar ta-baci a bangaren tsaro don magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.
A cewarsa, sojojin da za a yi amfani da su don aiwatar da irin wannan yanayin na gaggawa an riga an fadada su.
Don haka gwamnan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina sanya siyasa a cikin al’amuran tsaro, domin Sanya siyasa a sha’anin tsaro bazai haifarwa Kasar nan da Mai ido ba.
Ya ce ba za a bar Najeriya ta wargaje ba domin hakan na nufin babbar matsala ga nahiyar Afirka baki daya.
Masari, yayin da yake magana a kan fargabar cewa Kwamitin Raba Asusun Tarayya (FAAC) ba zai iya rarraba kason kudin na wata-wata na watan Mayu ba, ya kalubalanci hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da hanyar da za ta kau da hakan.