Rahotanni na nuni da cewa wata gobara ta tashi a Fadar masarautar Kano ta kofar kudu.
har yanzu dai ba‘a tabbatar da musabbabin afkuwar gobarar , wadda ta babbake guda cikin fadar sarkin Kano dake Kofar Kudu.
Binciken Yan sanda ya bayyana cewar gobarar ta faru ne da misalin karfe 11 na daren jiya Juma’a.
Rahotanni daga rundunar yan sanda a Kano sun bayyana cewar, an gano yadda aka lalata mukullin shiga fadar na baya amma ana cigaba da bincike, kamar yadda DW da DCL Hausa suka tabbatar.
DW.