Rikicin Sarautar Kano: Tinubu ya mayar da martani kan zargin shugaban NNPP

Date:

Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani game da wannan iƙirari na shugaban NNPP, tana mai cewa Shugaban Ƙasa Tinubu na da alaƙa mai kyau da duka ɓangarorin biyu “musamman ma Muhammadu Sanusi II”.

Ɗaya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Abdu’aziz Abdul’aziz ya ƙara da cewa maganar zargi ne kawai “maras tushe”.

“Abin da mai maganar bai sani ba ko kuma bai faɗa ba saboda siyasa shi ne; shugaban ƙasa na da alaƙa mai kyau da duka waɗanda ke taƙaddama a kan wannan sarauta,” in ji shi.

Talla

“Musamman ma Sarki Sanusi II, wanda suke da alaƙa tun lokacin da ya nemi sarautar a 2014. Kuma ya sani cewa Sarki Aminu Ado bai taɓa zuwa ya ga Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa ba tun lokacin da ya hau mulki.

Shugaban NNPP na Kano ya bayyana hujjar cewa Tinubu na da hannu a rikicin masarautar kano

“Amma Sanusi II ya zo ba sau ɗaya ba kuma ya ga shugaban ƙasa. Wannan ya nuna irin alaƙar da ke tsakaninsu. Wani mutum ya fito yana magana a kan wani abu da ba shi da hujja abin takaici ne.”

Ko a baya-bayan nan ma sai da musayar kalamai ta ɓarke tsakanin fadar Bola Tinubu da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa kwankwaso, kan zargin da Kwankwason ya yi cewar gwamnatin Tinubun na ƙoƙarin ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar Kano.

Yayin wani taron ƙaddamar da aiki da gwamnatin jihar Kano ta gudanar, an jiyo Kwankwaso na zargin cewa “wasu sun haɗa baki da jagororin jam’iyyar APC suna ƙoƙarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da fitina, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci”.

Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin marar tushe ballantana makama.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna...

Gwamnatin Kano ta bayyana sunayen unguwannin da aka sami gurbatacciyar Iska

    Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da...

Sallah: Gwamnatin Kano za ta hukunta gidan wasan da ya bar masu shigar banza da shaye-shaye

Daga Rahama Umar Kwaru   A kokarin ta na yaki da...

Sallah: Hussari ya sauke kabakin arziki ga yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale

Daga Ibrahim Abubakar Diso   Tsohon Dan Majalisar wakilai da ya...