Tsohon dan takarar mataimakin gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC a Jihar Kano, Alhaji Murtala Garo, ya taya al’ummar Musulmi murnar shigowa sabuwar shekarar musulunci ta 1446H.
Cikin wata sanarwa Alhaji Murtala Garo ya ce ya na fatan sabuwar shekarar za ta zama mai albarka ga al’ummar Musulmi a Jihar Kano da kasa baki daya.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kama aiki a mukamin da Tinubu ya bashi
“Ranar Lahadi ita ce daya ga watan sabuwar shekarar Musulunci ta 1446H kamar yadda Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya sanar.

“Ina taya al’ummar Musulmi na Jihar Kano da kasa baki daya murnar wannan rana mai albarka. Wannan rana ce mai matukar hamimmanci a duniyar Musulunci.
“Ina kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci dan habaka kaunar juna da jinkai tsakanin al’umma.
“Dukkan mu akwai rawar da za mu iya takawa dan gina al’umma da tabbatar da zaman lafiya kamar yanda addinin Musulunci ya koyar.”