Shugaban NNPP na Kano ya bayyana hujjar cewa Tinubu na da hannu a rikicin masarautar kano

Date:

Shugaban jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, Dr Hashimu Dungurawa ya zargi shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da hannu a hana ruwa gudu a rikicin masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Dr Hashimu ya shaida wa BBC cewa yana da hujjojin da ke gasgata zarge-zargen da ya yi, inda ya ce ” a bayyane take dangane da al’amarin da ke faruwa wanda kuma ke nuna sa hannun shugaban.”

” …Tinubu saboda alakarsa da mahaifiyar tsohon sarkin ƙwaryar birni, Aminu Ado Bayero, ya ce ba zai yarda ba dole sai an naɗa shi sarki. An kawo mana ƴan sanda da sojoji a birnin Kano a daidai lokacin da sauran sassan ƙasar suke fama da matsalar tsaro. Haka kawai saboda son ransa saboda cuzguna wa jam’iyyar da ba taka ba a jiha.” In ji Dungurawa.

Talla

Da BBC ta tambaye shugaban jam’iyyar ta NNPP na Kano dangane da hujjar da yake da ita kan zarge-zargen nasa sai ya ce ” wane ne shugaban ƙasar Najeriya a yanzu? Ba Tinubu ba ne? Yaya za a yi a jibge ƴansanda da sojoji na tsawon watanni ba tare da sanin shugaban ƙasa ba? Idan kuwa bai sani ba to akwai matsala.”

Ko Dungurawa ba ya tsoron a maka shi a kotu?

To sai dai shugaban jam’iyyar NNPP, Dr Hashim Dungurawa ya ce “ba na shakkar a kai ni kotu. To wace kotu ma za a kai ni bayan abun a fili yake ga duk wani mai hankali.”

Sabuwar shekara: Minista Gwarzo ya taya al’ummar Musulmi Murna

Ko a watan Mayu sai da mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam ya yi irin wannan zargi ga babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribaɗu, inda ya ce shi ne ke da hannu kan rikicin.

To sai dai bayan fitar da wata sanarwa daga ofishin Nuhu Ribaɗun da ke cewa za ta maka Kwamared Abdussalam a kotu bisa zarge-zargen nasa, sai mataimakin gwamnan ya fito kafafen watsa labarai ya janye kalaman nasa sannan ya nemi afuwar Ribaɗu cewa ya “samu bayanan ne ba daidai ba”.

Martanin fadar shugaban ƙasa

BBC ta tuntuɓi ɗaya daga cikin masu taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Malam Abdu’aziz Abdul’aziz kan zarge-zargen, to amma har lokacin fitar da wannan rahoto bai ce komai ba. Kuma da zarar fadar shugaban ƙasar ta mayar da martani za mu kawo muku.

Ko a baya-bayan nan ma sai da musayar kalamai ta ɓarke tsakanin fadar shugaban Bola Ahmed Tinubu ɗin da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa kwankwaso kan zargin da Kwankwason ya yi cewar gwamnatin Tinubun na ƙoƙarin ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Kano.

Yayin wani taron ƙaddamar da aiki da gwamnatin jihar Kano ta gudanar, an jiyo Kwankwaso na zargin cewa “wasu sun haɗa baki da jagororin jam’iyyar APC suna ƙoƙarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da fitina, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci”.

Sai dai fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin marar tushe ballantana makama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...