PDP ta taya Kwankwaso Murnar Cika Shekaru 65 a Duniya

Date:

Daga Halima M Abubakar
Uwar Jam’iyyar PDP ta Kasa ta taya tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso murnar cika shekaru 65 a duniya.
Cikin Wata sanarwa da Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na Kasa Kola Olugbondian ya Sanyawa hannu ya baina Sanata kwankwaso a Matsayin Wanda al’umma da dama Suka Amfana da Rayuwar Saboda irin matakan daya taka a rayuwarsa.
 Sanarwar ta ce Lokacin da kwankwaso yake Gwamnan Kano ya taimakawa al’ummar ta sannoni da dama Kamar ilimi, lafiya, Aikin Gona, da ma gudanar da manyan aiyukan Raya Kasa da Kano ba zata taba mantawa da su ba.
 A matsayinsa na jagoran siyasa, Sanata Kwankwaso ya kasance yana da kyakykyawar alaƙa da mutane, musamman a yunƙurin da suke yi na ganin sun ceto al’ummar Kasar nan daga halin kuncin da jam’iyyar APC da gwamnatinta ta Sanya al’umma a ciki.
 Jam’iyyar PDP na taya Sanata Kwankwaso murnar wannan gagarumin biki tare da yin addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kara masa shekaru masu yawa cikin koshin lafiya domin al’ummarmu za ta ci gaba da jan hankali daga jajircewa da jajircewa mai yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Za a kashe Naira Miliyan 87 wajen Sanya Interlock a sakatariyar K/H Dala – Surajo Imam

Daga Sani Idris Maiwaya   Gwamnatin jihar Kano ta Amince da...

Yansanda sun Haramta Hawan Sallah a Kano

Daga Abdulmajid Habib   Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta...

Sanata Barau ya kai ziyarar jaje ga iyalan ‘yan wasan da suka rasu, ya bayar da gudunmuwar N22m

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, a...

Hawan sallah : Sarki Sanusi ya umarci hakimai su shigo cikin birnin Kano

Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata takarda mai...