Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, kuma tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau ya kafe cewa Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam’iyyar APC zababbe na jihar Kano.
Tsohon gwamnan na Kano ya jaddada wannan matsayi nasa ne a wata sanarwa da ya fitar, sakamakon rabuwar kai da aka samu a zaben shugabannin jam’iyyar da ka yi a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba, 2021, inda aka yi zabe bangare biyu, wanda kuma har kawo yanzu uwar jam’iyyar ta kasa ba ta fitar da wata tartibiyar sanarwa kan shugabancin da ta amince da shi ba.
A yayin zaben na Asabar, bangaren gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zabi tsohon shugaban jam’iyyar wanda kuma har lokacin zaben yake matsayin shugaban riko, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar, yayin da bangaren Ibrahim Shekaru ya zabi Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban.
Sai dai kamar yadda muka ruwaito muku a baya, shugaban kwamitin da uwar jam’iyyar ta APC ta kasa ta tura jihar ta Kano domin gudanar da zaben Barista Auwalu Abdullahi, wanda ya jagoranci gudanar da zaben na bangaren gwamna a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata, ya bayyana cewa Abdullahi Abbas ne ya yi nasara da kuri’u 3,122.
Babban jami’in ya ce wannan ne ya bai wa Abdullahi Abbas din damar zama sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar ta Kano.
Bayan zaben na Asabar an ruwaito Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cewa sakamakon zaben babbar nasara ce ga jihar Kano, kuma sun san cewa a nan ne uwar jam’iyya ta aika wakilai har guda bakwai wadanda a kan idonsu komai ya gudana kuma sun tabbatar an yi zaben cikin gaskiya da adalci.
Gwamnan ya kara da cewa babu wasu jami’ai da aka tura wani wurin zabe na daban da aka yi, don haka nasu ne halattacce.
Sai dai daya bangaren wanda ke rikici da bangaren gwamnan na Kano, karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau din suma sun gudanar da nasu zaben a yankin Janguza da ke karamar hukumar Tofa a jihar ta Kano, inda suka zabi Alhaji Ahmad Haruna Zago a matsayin nasu shugaban jam’iyyar.