Daga Saddik Lamido Kurmawa
Sanatan da ke wakiltar gundumar sanata ta Kano ta Arewa a majalisar Dattijai ta kasa, Sanata Barau Jibrin ya ce shi dan siyasan ne da baya Zai yi tafiyar Ruwa da koma waye game da batun zaben Gwamnan Kano a 2023.
Sanatan ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labaran fadar Sarkin Kano jim kadan bayan ya yi wa mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsu Hajiya Maryam Ado Bayero.
Sanata Barau ya ce har yanzu lokaci bai yi ba na yakin neman zaben kujerar gwamna a 2023 a Kano, amma idan lokaci yayi za’a jini kawai yanzu babban aikin da yake gabana shi ne wakiltar al’ummar mazabata a majalisar kasa.
“Amma idan lokaci ya yi za ku san ni Bulldozer ne na siyasa, na bullo wa duk wanda ya zo wurina, tarihin siyasa na ya nuna cewa a shirye nake na yi nasara a kan abokan hamayyata a fagen siyasa, in ji sanata Barau Jibrin.
Lokacin da Najeriya ta koma kan mulkin dimokiradiyya a 1999 wasu gwamnoni da suka kammala wa’adin Mulkinsu na biyu su kan ba tikitin takarar gwamna ga sanatocin da ke wakiltar shiyyoyinsu kuma su kuma gwamnonin su karbi kujerun sanata.
Kadaura24 ta rawaito cewa Idan Mai karatu Zai iya tunawa akwai rade-radin Sanatan suna samun takun saka tsakanin sa da kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar Kano wanda ake ganin hakan tana faruwa ne saboda fafutukar zaben Shekara ta 2023.