Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murna ga tsohon Babban Darakta na Hukumar Hana Safarar Mutane, Sanata Basheer Garba Lado, bisa zagayowar ranar haihuwarsa, 16 ga Oktoba, 2021, inda jigon jam’iyyar ya cika shekara 55 a duniya.
Shugaba Buharin ya taya Murnar ne Cikin Wata sanarwa da Babban Mai taimaka Masa na Musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya aikewa Manema labarai.
Shugaban Kasar ya shiga sahun mambobin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), iyalan sanatan da abokan arzikinsa wajen taya shi murnar cika shekarar ne bisa la’akari da gudunmawarsa wajen cigaban kasa tun daga kuruciyarsa a matsayin dan kasuwa da kuma makaman da ya rike.
Bugu da kari, Shugaba Buhari ya yaba wa tsohon dan majalisar, wanda kuma ya taba rike mukamin Kwamishinan a Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, bisa sadaukarwarsa, da’arsa da mayar da hankalinsa da aka gani kuru-kuru a lokacin da ya ke Majalisar Dattawa da kuma jagoranci nagari da ya bayar a hukumomin da ya rike.
Sai Shugaban Kasar ya yi addu’ar Allah ya kara wa sanatan lafiya, ya kuma albarkaci iyalinsa.