Masana Zayyanar Kasa na da Gagarumar Rawar Takawa Wajen Ci gaban Nigeria – Ministan Gidaje

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Ministan gidaje da raya birane, Arc Ahmad Musa Dangiwa, ya yi kira ga kwararrun masana zayyanar kasa na Najeriya (Safayo) da su yi amfani da kwarewarsu wajen samar da kirkire-kirkire, ci gaba da kawo sauyi mai kyau a kasar.

Arc Dangiwa wanda ya samu wakilcin karamin ministan gidaje da raya birane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, ya yi wannan kiran ne a lokacin kaddamar da sabbin ma’aikatan safayo 485 wanda aka gudanar a otal din Chida dake Jabi a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce ƙaddamar da su wani abun alfahari ne da zai kara bunkasa da daga darajar safayo a Nigeria .

Mun dauki matakan shawo kan matsalar mai a Nigeria – NNPC

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban masharci na musamman ga karamin ministan Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Ministan ya shawarci sabbin masana safayon da cewa duk da cewa akai kalubale a gaban su, ya kamata su rika la’akari da ka’idojin aikin su da hada kai don cimma burin da aka sanya a gaba na hidimtawa al’umma da ta hanyar sana’ar su.

Sanarwa ta Musamman Daga Hukumar Samar da Ruwan sha ta Jihar Kano

Ya umurci manyan masana zayyanar da su dage wajen zaburarwa da ƙarfafa gwiwar sabbin masana zayyanar da aka ƙaddamar domin inganta aiyukan su.

A wajabinsa tun da farko, Babban Sufayon na kasa , Surveyor Abuduganiyu Adeyemi, ya ce masu zayyanar kasa suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kowace kasa.

Babban safiyon ya bukaci sabbin masana zayyanar da su kasance masu koya nema sani a wajen wadanda suka fi su sani, kuma su kasance jakadun na gari domin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...