Daga Abubakar Sa’eed Suleman
Gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka aikowa Kadaura24 a ranar Larabar Nan.
Ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ba da wannan umarnin ne yayin taron Majalisar Zartarwa na mako-mako da ake gudanarwa a Fadar Afirka, gidan Gwamnati, Kano.
Malam Garba ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan nasarorin da aka samu a yaki da cutar ta COVID-19 a cikin jihar a cikin watanni uku da suka gabata.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, Manyan sakatarorin da shugabannin sassa a Ma’aikatansu da hukumomi ana basu Umarnin dasu tabbatar da cewa an bin ka’idoji da dokokin gwamnati na COVID-19 a wuraren ayyukansu.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito An umarci Ma’aikata a Kano da su kasance a gida tun ranar 18 ga watan Janairu, sakamakon bullar cutar.
Allah ya yaye mana wannan musifar Covid 19