Daga Abubakar Lawan Bichi
Karamar hukumar Bichi ta rushe dukkanin kwamitocin lafiya na Asibitoci dana Ilimi da kuma na hakar ma’adai a garin Danzabuwa dake Karamar hukumar ta Bichi.
Da yake rushe Kwamitoci Shugaban riko na Karamar hukumar Alhaji Ahmad Kado Bichi yace an rushe Kwamitoci bisa Kyakyakyawan manufa sakamako kiraye kiraye da Jama’a suke dan kawo sabon Cigaban a dukkan fadi Karamar hukumar ta Bichi.
Yanzu-yanzu: Muhuyi Magaji Ya Sake Kaddamar da Sabbin Zarge-zarge akan Ganduje
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na Karamar hukumar ta Bichi Mukhtar Usman Romi ya aikowa kadaura24 a ranar talata.
Dan haka Alh Ahmad Kado Bichi ya bukaci russusun yan Kwamiti dasu mika kayan aiki ga Karamar hukumar ta Bichi.