Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wasu daga cikin yan masana’antar kannywood suna cigaba da tufa albarkacin bakin su kan kalaman da jarumi Adam A zango yayi a daren ranar lahadin da ta gabata .
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Adam A zango ya zargi yan Kannywood da hassada , kiyashi da kuma Rashin tsayawa don taimakon junansu musamman wadanda yace ya taimakawa har suka kai Inda suka kai a yanzu.
Daga Cikin wadanda suka yi tsokaci akan kalaman da Adam A zango akwai :
Ali Jita
Ali jita Wanda guda ne cikin wadanda Adam Zango yace ya taimakawa a masana’antar ya fito cikin wani bidiyon ya tabbatar da cewa tabbatas Adam Zango ya taimaka musu, Amma suna bashi hakuri kan abun da ya faru.
“Ina magana ne a madadin Abubakar Sani da Nazifi Asnanic tabbatas Adam Zango ya taimaka mana a wannan harkar kuma abubunwa da dama sun faru, don haka muna masu baiwa Adam Zango Hakuri, kuma idan ya dawo zamu zauna da shi don kara bashi hakuri da kuma yadda zamu shigo cikin matsalarsa”. Inji Ali Jita
Tsohon Mawaki Muddassir Kasim
NI SHAWARAR DA ZANBA WANNAN DAN TALIKI ITACE:
a) ya daina magana akan rayuwar sa a social media.
b) A maimakon haka ya kirkiri content mai script da aka yi da ilimi ya rinka yi a shafukan sa amma ya daina magana out of script.
(To tunda a social media ya yi magana shiyasa zan bashi Shawara a social media da shi da ire-iren sa, domin har yanzu akwai ragowar dabi’ar nan ta kin daga waya)
1) Da zai yarda cewa daukaka ta Allah ce kuma irin waccan daukakar da ya samu ta barshi saidai abinda ba’a rasa ba, kuma hukuncin Allah ne ba wani ba, to zai samu lafiya da nutsuwa a matakin farko.
2) Da zai koma makaranta ya kara neman ilimi musamman na addini a zamanance da zai samu natsuwa.
3) Da zai sauko da kanshi ya samu mashawarta dattijai masu hankali da hangen nesa, masana akan dabia’ar zamantakewar ma’aurata kuma ya yarda da kuskuren sa sannan ya yarda da shawarar da zaa bashi wajen samun matar da zai aura da gyaran rayuwar shi, to da zai dawo daidai.
4) Da zai fita daga sabgar yan kannywood cewa lallai sai sun yi masa yadda suke masa a da sanda ludayinshi ke kan dawo, da zai samu nutsuwar zuciya, domin yan kannywood suna yi ne kawai da wanda ake yi da shi, idan an Barka suma zasu Barka ne koda ko zaka yita ihu bazasu jika ba, saidai inka mutu suyi alhinin kwana 3 bayan sun binne ka. Wannan kuma haka yake a kowani irin sha’ani na al’umma ba wai a Kannywoodtoday Kannywood ne kaɗai ba
5) Da zai gyara dabi’un da ya rinka yi sanda yana kan sharafin sa ya yarda cewa tabbas ya yi kuskure ya dawo ya gyara a sauran ‘yar damar da ta rage masa to da zai ga chanji mai yawa insha Allah.
Wannan Ni ita ce nasiha ta gareahi. Allah ya sa sako na ya kai gare shi.
Ita kuma marubuciya a masana’antar kannywood Fauziyya D Sulaiman ga nata tsokacin
Fauziyya D Sulaiman
DON ALLAH MU TAIMAKAWA ADAM ZANGO DA SOYAYYA A HALIN DA YA KE CIKI A YANZU
Ban taba magana akan wani dan fim ba, amma halin da Adam Zango ke ciki yana bukatar mu nuna masa soyayya irin ta addini, yana bukatar mu ja shi a jiki, abubuwan da ya ke yi a yanzu akwai damuwa, don Allah a samu wadanda za su je kusa da shi don Allah, komai zai iya faruwa da shi, domin a tanzu yana ruguza gidansa da rayuwar yaransa da danginsa da ‘yan’uwansa.
Amma don Allah mu ka ja shi a jiki kar mu ji haushinsa yana bukatar kulawar duk wani musulmi hakan zai dawo da shi daidai ya fita daga danuwar da ya ke ciki, mu yi hakuri mu kawar da kai ga komai, don Allah a samu masu ziwa kusa da shi please kafin abunnan ya gama lalacewa.
Daddy Hikima ( Abale)
Shi ma kusa irin shawarar da Fauziyya D Sulaiman ta bayar irin ta ya bayar ta a jawo Adam Zango a jiki a zauna da shi a ji macece matsalarsa sannan a nemi hanyoyin Magance su.
Ali Nuhu
Shi kuma jarumi Ali Nuhu cewa yayi adam zango lafiyarsa lau, wasu lokutan mukan yi fushi saboda kasancewarmu yan Adam, Mun gode da kulawa da addu’o’inku . Mun ji dadi sosai mun gode.