Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Iyalan shehun Malamin Addinin Musulunci nan a Nigeria Sheikh Dahiru Bauchi sun karyata jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta na rasuwarsa.
KADAURA24 ta lura cewa a yan Kwanakin da suka gabata anyi ta samun cece-kuce game da lafiyar Sheikh Dahiru Bauchi a shafukan sada zumunta a makon jiya.
Bayanan da Iyalai da almajiran shehun Malamin sun tabbatar da lafiyar Sheikh Dahiru Bauchi, tare da sanya sabon hotonsa don tabbatar da cewa yana nan a raye.
Dan majalisar dokokin jihar kano Ibrahim kundila ya rasu
Malam Abdullah Sheikh, daya daga cikin ‘ya’yan malamin, wanda ya karyata jita-jitar a sahihin shafin sa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce “Maulana Sheikh na cikin koshin lafiya. A yau ne zai dawo Bauchi daga Abuja; zai dawo gida yau da yamma.”
” Makiyan Malam ne kawai suke kitsa labarin na Karya Saboda basu da abun yi”. Inji shi
Ku Fara Neman Watan Shawwal A Gobe Litinin – Sarkin Musulmi Ga Musulmin Nigeria
Wani almajirin Shehin Malamin, Abubakar Ibrahim Wunti, wanda shi ma ya yi watsi da jita-jitar ya ce “Sheikh Maulana Dahiru Bauchi yana raye. Yau zai dawo daga Abuja zuwa Bauchi saboda bai je ummarah ba a bana .”
Ya bayyana cewa, “Abin da Shehin Malamin yake fama da shi shi ne tsufa ba ciwo ba, kuma a kullum muna rokon Allah Ya kara masa lafiya, kuma Allah Ya yi mana maganin masu yada labaran karya akan shehun mu”.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito wannan ba shi ne karon farko da ake yada jita-jita a shafukan sada zumunta ba, game da mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi wanda labarin nasu ba shi da tushe balle makama.