Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibrin Ismail Falgore ya tabbatar da bukatar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf na samar da sabbin ma’aikatu a jihar.
Shugaban majalisar ya ce an sanar da shi ne ta hanyar wata wasika da gwamna Yusuf ya aikewa majalisar dokokin jihar, inda ya bayyana aniyar gwamnatinsa na kafa sabbin ma’aikatu a jihar.
Gwamnan Kano ya turawa majalisa sunan dan Kwankwaso da mutane 3 domin nada su Kwamishinoni
Rt. Hon. Falgore ya karanta wasikar a gaban ‘yan majalisar, inda ya ambato gwamnan ya bayyana cewa kafa ma’aikatun da ake son kafawa na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsa na inganta ayyuka a jihar.
Dr. Gumi ya bayyana abubunwan da suka tattauna da jami’an tsaron Nigeria
Ma’aikatun da aka gabatarwa majalisar domin kafawa sun hada da ma’aikatar harkokin jin kai da kawar da talauci da ma’aikatar Ma’adanai da sabbin makamashi sai kuma Ma’aikatar Tsaron cikin gida na ciki da aiyuka na Musamman.
A cewar gwamnan, sabbin ma’aikatun za su taka rawar gani wajen inganta harkokin zamantakewa da tattalin arziki da samar da shugabanci na gari tare da sanya jihar a kan wani tsari na ci gaba mai dorewa.