Gwamnan Kano ya turawa majalisa sunan dan Kwankwaso da mutane 3 domin nada su Kwamishinoni

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya turawa majalisar dokokin jihar sunayen mutane 4 wadanda yake son nada su a matsayin kwamishinoni a kunshin gwamnatinsa .

Kadaura24 ta rawaito Shugaban Majalisar Jibril Isma’il Falgore ne ya karanta sunayen a zauren majalisar a yau talata.

Gwamnan ya bukaci majalisar ta tantance tare da amince masa ya nada wadanda sukai musu Sunayen domin ya nada su a matsayin kwamishinoni.

Yanzu-yanzu: Kotu ta Yankewa Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Hukunci

Ga Sunayen Wadanda za’a nada din kamar haka:

1. Mustapha Rabi’u Kwankwaso

2. Adamu Aliyu Kibiya

3. Usman Shehu Aliyu Karaye

4. Abduljabbar Garko

Dr. Gumi ya bayyana abubunwan da suka tattauna da jami’an tsaron Nigeria

Mustapha Rabi’u Kwankwaso dai da ne ga jagoran Kwankwasiyya kuma ubangida gwamnan Kano wato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Shi kuma Adamu Aliyu Kibiya shi ne tsohon kwamishinan kasa da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya dakatar lokacin da ake shari’ar zaɓen gwamnan jihar kano, sakamakon wasu kalamai da yayi kan alƙalai.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a Kwanakin bayan gwamnan ya bada umarni ga kwamishinoninsa da su cike wani fom domin gano masu kwazo da marasa kwazo cikin Kwamishinonin, inda yayi alkawarin chanza duk kwamishinan da bai yi kwazo ba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...