Daga Nura Abubakar
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba zai rattaba hannu a kan kudirin dokar da zata baiwa bangaren shari’a yancin cin fashin Kai a jihar Kano ta shekarar 2021.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne yayin bikin makon Kungiyar Alkalai ta kasa (MAN) na shekarar 2021, wanda aka gudanar a Coronation Hall, dake Gidan Gwamnatin Kano.
Ya bayyana cewa yana farin ciki da Wannan taron Saboda ya zo a dai-dai lokacin da gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf don karba da Sanya hannu a dokar cin gashin Kan bangaren Shari’a da zarar Majalisar Dokokin jihar kano ta Amince da ita.
Ganduje ya ba da tabbacin cewa, da zarar majalisar dokokin jihar ta Amince da Kudirin, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da shi tare da fara aiwatar da dokar ba tare da bata lokaci ba.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin cin gashin kai tare da tabbatar da aiwatar da cin gashin kai ga bangaren shari’a.
Gwamna Ganduje ya yi alkawarin cewa, jihar ta umarci Ma’aikatar Kudi da ta saki kudade ga Ma’aikatar Shari’a don halartar Babban taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ga Alkalan Majistare da Alkalan Kotun Shari’a da Kuma reshen Kungiyar na Jiha.
Gwamnan ya bayyana cewa, jihar za ta saki jimlar Naira Miliyan Dubu Takwas (N800,000,000), don sayan motoci ga bangaren wanda Kuma Majalisar Zartarwar ta jihar Tuni ta Amince da a fitar da kudaden.