October 20, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Kungiyar yan awaren Inyamurai ta IPOB Ta hana sayar da tsire a yankinsu

Tsagerun kungiyar Inyamurai ta IPOB ta fitar da wata sanarwa ta haramta sayarwa ko cin tsire a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

 

A cewar sanarwar da kungiyar ta fitar, daga watan Afrilun shekarar 2022 ba zasu sake bari mutanen yankin suci tsire ko su bari a dinga sayar da shi ba, a cewarsu, sun dau wannan mataki ne don nuna fushinsu kan yadda ake tsangwamar ‘ya ‘yan kungiyar dake neman ballewa dan kafa kasar Biyafara.

 

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito Kungiyar dai ta jima tana sanya dokar hana mutane walwala tare da tilasta musu zaman gida, kuma mutane suna bin umarnin duk kuwa da kiraye- kirayea da gwamnatocin yankin suke yi na cewa jama’a suyi watsi da sanarwar ta ‘yan awaren su fito suyi harkokinsu, amma mutane sun fi tsoron ‘yan IPOB.