October 19, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Yanzu-Yanzu: Malamai a Kano sun cire Sheikh Ibrahim Khalil Daga Shugabancin Majalisar Malamai

Daga Halima M Abubakar

 

Gamayyar kungiyoyin Malaman jihar Kano sun bayyana Cewa sun tsige Shugaban Majalisar Malaman ta Kano Sheikh Ibrahim Khalil Daga Shugabancin Majalisar bisa Wasu laufuka da suke tuhumar shehun Malamin.

 

Cikin Wata sanarwa da Ustaz Saifullahi Adam Assudani da Sheikh Khalifa Gama da sheikh Abdulkadir Ramadan da Kuma Imam Jamil Abubakar suka Sanyawa Hannu sun ce sun dauki Wannan Matakin ne da yawun dukkanin Malaman jihar Kano.
Sanarwar tace malam Ibrahim Khalil ya Gaza ciyar da Majalisar gaba,Sannan Suka ce Majalisar Bata aikin da aka dora Mata na yin Fatawa ga al’umma Kan sabbin Matsalolin da suke bijirowa a Wannan zamanin.
Suka ce yana Amfani da ofishin Majalisar Wajen taroka na kashin Kansa ba na Majalisar ba,  ya Gaza Kade Kan bangarorin Izala Qadirriyya da Tijjaniya a Kano Sannan Kuma Suka ce ya shiga Siyasa harma takara yake nema.
Sanarwar yace bisa Wadancan dalilai ne yasa dukkanin malamai daga bangaren Tijjaniya, Qadirriyya da Izala duka ga dacewar su sauke shi daga Shugabancin Majalisar, sai dai sun ce garanbawul din da aka yiwa Majalisar Shugaban Kadai ta shafa sauran Shugabanin Suna nan akan mukamansu.
Daga Karshe Sanarwar ta bayyana Cewa sun zabi Farfesa Abdullah Saleh Pakistan a Matsayin Sabon Shugaban Majalisar Malaman jihar Kano Kuma sun ce kowa daga kowanne bangare na Tijjaniya, Qadirriyya da Izala sun Amince da Wannan Mataki.