Daga Samira Hassan
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayar da umarnin raba man dizal ga dukkan rijiyoyin burtsatse da ke Damaturu da kewaye domin saukakawa al’umma matsalar karancin ruwa da suke fuskanta a ‘yan kwanakin nan.
Wannan umarnin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na SSG Baba Malam Wali mni, Shu’aibu Abdullahi ya aikowa jaridar kadaura24 a Damaturu ranar Lahadi.
Gwamna Buni Ya Sami Gagarumar Nasara a Bangaren Ilimi da Lafiya a Yobe – Baba Malam Wali
Gwamnan ya ce akwai isashen man dizal da za a raba domin samar da wutar lantarki ga dukkan rijiyoyin burtsatse a yankunan da abin ya shafa, inda ya yi alkawarin za a magance matsalar ba tare da bata lokaci ba.
Mazauna garin Damaturu da kewaye suna fuskantar matsalar karancin ruwan sha sakamakon lalata layin wutar lantarki mai karfin 330kv da wasu barayi suka yi.
Hakan ya sanya al’ummar yankin suke wahala, sakamakon dukiyoyin burtsatse duk suna amfani da hasken wutar lantar, hakan tasa gwamna Buni ya dauki matakin raba musu man dizal don saukakawa al’ummar yankin.