Kotu ta rushe Shugabanin rikon APC a kwara

Date:

Babbar kotu ta yanke hukuncin rushe shugabannin riko da gwamnan Kwara ya naɗa a kananan hukumomi 16 na jihar

Kotun tace babu dalilin da zai sa gwamna ya rushe zababbun ciyamomi, kuma ya maye gurbinsu da kantomomi.
Jam’iyyar adawa PDP ta bayyana jin daɗinta kan matakin kotun, inda tace wannan nasara ce ga mulkin demokaraɗiyya.
Kwara – Babbar kotun jihar Kwara ta rushe kwamitin rikon kwarya da gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya naɗa domin su jagoranci kananan hukumomi 16 dake jihar.
Premium times ta ruwaito cewa gwamna AbdulRazaq ya naɗa shugabannin riko a ƙananan hukumomin jihar bayan dakatar da zababbu.
Amma a ranar Jumu’a, Mai shari’a Hassan Gegele, na babbar kotun jihar dake zama a Ilorin, ya bayyana matakin da gwamnan ya ɗauka da, “cin mutuncin mulki.”
Gegele ya yi hukunci ne kan ƙarar da wata ƙungiyar al’umma ta shigar a gabansa, tana ƙalubalantar naɗa kwamitin riko da gwamnan jihar ya yi.
Shin gwamnatin Kwara ta amince da hukuncin?
Da yake martani kan hukuncin kotun, Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a, Salman Jawondo yace gwamnati zata ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
“Muna tabbatar da cewa shari’a kan wannan lamarin ba ta kare ba, domin zamu ɗaukaka ƙara zuwa kotun Allah ya isa.”

16 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...