Bana goyon bayan cakuduwa tsakanin Maza da Mata a wajen Maulidi – Sheikh Nasir Adam

Date:

Daga Nura Abubakar

Shugaban Majalisar Limaman juma’a ta jihar Kano Kuma babban Limaman masallacin Juma’a na Sheikh Ahmadu Tijjani dake Kofar mata Sheikh Nasir Adam ya bayyana Cewa baya goyon bayan cakuduwar da ake yi tsakanin Maza da Mata a wuraren Maulidi.
Sheikh Nasir Adam ya bayyana hakan ne wajen Maulidin da Zawiyyar Marigayi Uba Ibrahim Ringim dake unguwar sabuwar kofa a birnin Kano.
Shehun Malamin yace ya Zama wajibi Malamai su Rika kula sosai wajen tabbatar da Mata basu hadu da Mata ba,Inda yace sau tari anfi Samun irin Wannan mummunar Dabi’ar Yayin da Dalibai suke zagayen kewaye Gari a Wannan Wata na Maulidi.
” Wannan mummunar Dabi’ar gaskiya tana neman Kara yawa a Cikin al’ummar mu ,Kuma hakan ba karamin kuskure bane Wanda hakan kan baiwa shedan da shedanun Mutane damar aiwatar da wancan shedanci a warwaren wancan zagaye.”
Sheikh Nasir Adam ya bukaci Iyayen yara da malaman makarantu dasu tashi tsaye wajen yakar Wannan mummunar Dabi’ar wadda take Kara Shigar al’ummar mu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...