Iftila’i: Wani Soja ya Bankawa kansa wuta

Date:

Hukumomi a Washington sun ce wani soja ya cinna wa kansa wuta a gaban ginin ofishin jakadancin Isra’ila ranar Lahadi.

Mutumin wanda ba a tantance ba, an bayyana cewa yana cikin mawuyacin hali a asibiti.

Mai magana da yawun sojin Amurka ta tabbatar da faruwar lamarin.

Wakilin BBC ya ce wannan dai ba shi ne karon farko ba da hakan ke faruwa a bakin ofishin jakadancin Isra’ila ba a Amurka tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Hamas da Isra’ilar.

Zargin Juyin Mulki: Helkwatar tsaron Nigeria ta Magantu ta Batu

Ko a watan Disambar bara wani ya aikata hakan a jihar Georgia.

Wani bidiyo ya ɓulla a shafukan sada zumunta inda a ciki aka ga mutum na ihu da cewa “A ƴanta Falasɗinu” yayin da yake ƙonewa, kamar yadda rahoton kafofin yaɗa labaran Amurka ya ce.

An tura jami’an sashen kwance bom zuwa wurin kan fargabar da aka yi game da wata mota da ake iya alaƙantawa da mutumin.

Daga bisani an bayyana cewa ba a gano wasu abubuwan hadari ba a cikin motar.

Kungiyar Kwadago ta bayyana matakin da zata dauka idan aka kaiwa ya’yanta hari yayin zanga-zanga

Ba a sami wani ma’aikacin ofishin jakadanci ba da ya ji rauni, kamar yadda mai magana da yawun ofishin jakadancin ta shaida wa jaridar New York Times.

Cikin wata sanarwa, ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ce ma’aikatan ofishin jakadancin ba su san mutumin ba.

Ƴan sanda sun ce mutumin ya yi amfani da fetur sannan an ga tutar Falasɗin a wajen da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...