Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitocin kar-ta-kwana don kula da haramtattun gine-gine, da kuma gine-gine da aka yi su ba tare da izini ba tare da kwacesu.
Manajan Darakta na Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Arch. Ibrahim Yakub Adamu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da Jama’a ta ma’aikatar Bahijja Malam Kabara ta aikowa kadaura24.
Zanga-Zangar NLC: Kungiyar Yarbawa Ta Baiwa Yan Kabilar Umarni
Manajan daraktan ya bayyana dalilan kaddamar da kwamitocin da suka yi daidai da kishin Gwamnati mai ci na ganin Kano ta zama ta daya a tarayyar Nigeria a fannin tsara burane.
Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da yin gine-gine da kuma sayar da su ba tare da amincewar KNUPDA ba, yana mai gargadin cewa gwamnatin yanzu ta Alhaji Abba Kabir Yusuf za ta dauki matakan da suka dace a kan masu karya dokokin gwamnati.
Junaid Abdullah ne zai ya jagoranci kwamitin yayin da membobin suka haɗa da duk daraktoci da wakilan kamfanoni masu zaman kansu dake samar da rukunin unguwanni a Kano.
Marubucin Fim din Labarina Ya yiwa yan kallo Martani game da Shirin na Wannan makon jiya
A nasa bangaren Tpl Junaid Abdullahi ya bayyana cewa a shirye su ke su yi aiki tukuru domin cimma burin da ake so.
Shugaban ya kuma bukaci jama’a da su rika tuntubar masu unguwanni da hakimai da sauran masu ruwa da tsaki kafin su sayi duk wani fili.
Yankunan da suka ziyarta sun hada da Yankatsari a karamar hukumar Dawakin Kudu, Kumbotso, Gezawa da Nassarawa.