Gwamnatin Nigeria za ta yi maganin masu yi wa kasuwar chanji zagon-ƙasa – Ministan yada labarai

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta riƙa kama ɗaiɗaiku da kamfanonin da ke yin canjin kuɗi ta haramtacciyar hanya da kuma ma su yi mata zagon ƙasa.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’uma na Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka a wani taro da aka shirya kan sabbin hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu ya ɓullo da su.

Shugaban ƙasar dai ya fito da manufofin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da suka haɗa da cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta yi wa naira farashi.

Tinubu Ya Bayyana Hanyoyin Da Za’a Daidata Tsakanin ECOWAS Da Nijar Burkina Faso da Mali

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan ya ce Babban Bankin Kasar yana iya ƙoƙarinsa wajen samar da hanyoyin wadata kasuwar canji da garin kudi, yana cewa masu zagon-ƙasa na ta yi wa shirin CBN ɗin ƙafar-ungulu.

“A matakin daidaita farashi CBN zai samar da wadatacciyar dala sannan ya fitar da sabbin hanyoyin hada-hadarta ga bankunan kasuwanci da kuma ‘yan kasuwar chanji,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...