Muhimman Abubuwa 6 da aka tattauna tsakanin Tinubu da Gwamnonin Nigeria

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

A safiyar yau (Alhamis) ne shugaban kasa Bola Tinubu tare da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya gana da gwamnonin jihohi 36 da kuma ministan babban birnin tarayya Abuja.

Taron dai ya cimma matsaya guda domin tinkarar wasu kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu, musamman tsadar abinci da rashin tsaro.

Bayan tattaunawa mai zurfi shugaban kasa da gwamnonin sun amince da yin aiki tare don magance matsalolin da kuma magance matsalolin tattalin arzikin da ‘yan kasar ke fuskanta.

A Wata sanarwa da babban mataimaki na Musamman ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ya aikowa kadaura24, yace an cimma mahimman batutuwa 6 a karshen taron:

Da dumi-dumi: Kotun Shari’ar Musulunci ta Kwace Kaddarorin Sha’aban Saboda Bashi

1. Akan magance matsalar rashin tsaro wanda ke shafar noma da samar da abinci, shugaba Tinubu yayi maganganu guda 3.

A. Za a dauki karin jami’an ‘yan sanda domin karfafa rundunar.

B. Shugaba Tinubu ya sanar da Gwamnonin cewa Gwamnatin Tarayya za ta hada kai da su da Majalisar Dokoki ta kasa wajen samar da wata hanya da za ta haifar da ‘yan sandan Jihohi maimakon ‘yan banga da ake amfani da su a wasu Jihohin.

C. Shugaban ya bukaci Gwamnonin da su karfafa gwiwar masu kula da gandun daji tare da ba su makamai domin kare dukkan dajin daga masu aikata laifuka.

Hanyoyin da ‘yan sandan jihohi za su bi da kuma magance matsalolin tsaro da za a ci gaba da tattaunawa a majalisar tattalin arzikin kasa.

Aminu Dantata ya Bayyana Ra’ayinsa Kan Batun Sauya Tsarin Shugabanci a Nigeria

2. Akan tsadar kayan abinci: Shugaban ya ba da umarnin cewa gwamnatocin Jihohi da gwamnatin tarayya su hada kai don kara samar da abinci a cikin gida. Shugaban ya ba da shawarar a daina tunanin shigo da abinci da kuma kula da farashin lokacin da ya kamata a karfafa gwiwar masu samar da abinci na cikin gida don su kara samar da abinci.

3. Shugaban ya shawarci Gwamnoni da su yi koyi da jihar Kano wajen yakar yan Kasuwar dake boye kayan abinci don cin kazamar riba . Ya umurci Sufeto-Janar na ‘yan sanda, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ma’aikatar harkokin tsaro ta kasa da su sanya ido kan rumbunan adana kayan abinci a fadin kasar nan .

4. Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnonin da su mai da hankali wajen bunkasa kiwon dabbobi a jihohinsu da kuma kara yawan noma musamman na kaji da kifi.

5. Shugaban ya roki Gwamnoni da su tabbatar da cewa sun biya duk wasu hakkoki da ma’aikatansu da na kuma ‘yan fansho tunda yanzu jihohi suna samun karin kudaden shiga na FAAC duk wata.

6. Shugaba Tinubu ya roki Gwamnoni da su kara samar da guraben ayyukan yi ga matasa a jihohinsu domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...