Aminu Dantata ya Bayyana Ra’ayinsa Kan Batun Sauya Tsarin Shugabanci a Nigeria

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Shahararren dan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata, ya ce tsarin Firaminista da wasu ‘yan majalisa ke Kokarin tabbatarwa shi ne mafi alheri ga Nigeria n.

Dantata ya bayyana haka ne a lokacin da wasu ‘yan majalisar wakilai karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, suka kai masa ziyarar neman shawara a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis.

Yadda Yan Majalisa ke Kokarin Mayar da Nigeria Tsarin Firaminista

Daily Trust ta rawaito cewa Dantata ya ce, “Na gode kwarai da zuwan ku gidana: Ina yi wa wannan gagarumin yunkuri naku fatan nasara.

“Tsarin Firaminista ya fi kyau ga kasar nan saboda yana da arha sosai yayin da tsarin shugaban kasa mai cikakken iko yake da tsada sosai musamman ga kasa kamar Nigeria.

Sarkin Musulmi ya bayyana dalilansa na cewa Najeriya tana kan tsini

“Ina fatan zaku sami hadin kan abokan aikinku kuma ina rokon Allah Ya ba ku hikima ya kuma yi muku jagora don cimma wannan kyakkyawan aiki na taimakon kasar nan.”

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito wasu yan majalisu kusan su 90 sun nuna goyon bayamsu kan wannan yunkurin na mayar da Nigeria Tsarin Firaminista a jamhoriya ta Farko da kuma kafin kasar ta sami yancin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...