Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa, NAFDAC, a jihar Kaduna ta rufe wasu cibiyoyi hudu da suke aikin samar da madarar yogot ba tare da rajista ba.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nasiru Mato ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a Kaduna.
Mato ya ce hukumar ta rufe wuraren ne yayin da take zagayen Sanya idonu a jihar don bankado Masu Aiki ba bisa ka’ida ba Kamar yadda Wadancan suke yi. Yace sun same su Suna aiki da kayiyaki mass inganci, rashin tsaftar muhalli, da aiki da tsohon lasisin da wa’adin su ya kare.
Ya ce aikin sa ido wani bangare ne na matakan da hukumar ta ke dauka a jihar don tabbatar da cewa kmafanoni Suna Amfani da Sinadarai Masu inganci da tsafta da dai Sauransu.
“Dangane da abin da ya gabata, muna so mu yi amfani da wannan damar don jaddada cewa dole ne a kiyaye tare da bin ƙa’idojin aiki ga masu samar da yoghurt da sauran abubuwan sha na ruwa don kare lafiyar masu amfani da su.