Yan Sanda sun ceto Mutane 180 da Yan Bindiga suka sace a Zamfara

Date:

Rundunar ‘yan sanda jihar Zamfara ta sanar da ceto sama da mutum 180 wadanda ‘yan fashin daji suka sace a kauyukansu.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Mohammed Shehu, ya fitar ya ce mutanen sun shafe makonni a hannun ‘yan fashin dajin.

An yi nasarar ceto mutanen ne bayan wani aikin nema da ceto da jami’an tsaro suka yi a dajin Tsibiri da ke karamar hukumar Maradun a jihar ta Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce tuni aka mika mutanen hannun jami’an gwamnati domin kai su asibiti a duba lafiyarsu.

Kanhaka BBC ta tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara don jin a irin halin da aka samu wadannan mutane da aka ceto.

Ibrahim Dosara, ya ce an same su cikin yanayi na galabaita sosai, domin da yawa daga cikinsu an same su da ƙuraje a jikinsu saboda cizon sauro da makamantansu.

Ya ce, “Wasu daga cikin mutanen kuma saboda wahalar da suka sha ko tafiya ba sa iya yi sai an rike su, sannan kuma mata sun fi maza yawa a cikin mutanen. Kwamishinan ya ce, da zarar an kammala duba lafiyarsu za a kai su domin sada su da iyalansu.

Mahukunta a Zamfara na ci gaba da zafafa kai hare-hare kan ‘yan bindiga a dazukan Zamfara da Katsina da kaduna.

Haka kuma a baya bayan nan jihohin Zamfara da Kaduna suka katse layukan waya domin ba wa jami’an tsaro damar yaki da ‘yan fashin dajin.

Matsalar satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da kamari musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, duk da ikirarin da gwamnatoci ke yi na samun galaba a kan masu satar mutanen.

A shekarar 2021 kadai, an sace fiye da dalibai 1,000 daga makarantansu, abin da ke sanya fargaba a zukatan iyayen yara a kan makomar ilimi a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...