Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ta na kafa hukumar kula da kayayyakin Abinchi ta kasa a matsayin mafita ga hauhawar farashin kayan masarufi a kasa Nigeria.
*A kokarin magance matsalar hauhawar farashin, za a baiwa hukumar aikin tantancewa da daidaita farashin abinci, da kuma kula da dabarun adana abinci don daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinchi”.
Mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin wani babban taro na kwanaki biyu kan sauyin yanayi, tsarin abinci da kuma tattara albarkatu, wanda aka gudanar a dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa, Abuja.
Yan Hisbah a Kano Sun Kama Tauraruwar TIKTOK
Da yake gabatar da jawabinsa mai taken, “Tsarin yanayi da Samar da wadataccen Abinci”. Kashim Shettima ya ce taron na kwanaki biyu shaida ne kan kokarin da Najeriya ke yi na dakile illolin sauyin yanayi da kuma tabbatar da wadatar abinci ga ‘yan Najeriya.
“Don Maganin matsalar karancin abinci da za a iya fuskanta akwai bukatar daukar matakan gaggawa, da yin shiri na dogo matsakaici da gajeren zango, Wanda zai mayar da hankali wajen farfado da samar da abinci ta hanyar wasu ayyuka na musamman kamar rarraba takin zamani da hatsi ga manoma da gidaje don magance matsalar da cire tallafin man fetur ya haifar. Samar da hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar noma da ma’aikatar albarkatun ruwa domin inganta noman rani da samar da abinci a duk shekara, da magance hauhawar farashi ta hanyar kafa hukumar samar da kayayyaki ta kasa.
Da dumi-dumi: Kotu ta Haramtawa Gwamnatin Kano Rusau
“Wannan hukumar zata ci gaba da kula tare da kaiyade farashin abinci, tare da kiyaye dabarun adana abinci a Nigeria,” in ji Shattima
- Shattima ya ba da tabbacin cewa, gwamnatin Tinubu ta na da shirin dawo da “kadada miliyan hudu, ko kusan eka miliyan 10, don inganta noma a fadin Kasar.
Dangane da yadda gwamnati ke tinkarar kalubalen tsaro da ya hana manoma yin aikin gona a gonakinsu, ya ce, “Ina so in tabbatar muku da cewa za mu samar da jami’an tsaro don kare gonaki da manoma domin manoma su koma gonakinsu ba tare da tsoron hare-hare ba.