Naburaska ya Magantu Kan Masu Kokarin Hana shi Shirya fim din IGIYAR ZATO

Date:

Daga. Aliyu Danbala Gwarzo.

 

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kanneywood wato Alhaji Mustapha Badamasi wanda akafi sani da Naburska, yace ko kadan bai taba tsorata da barazanar da ake nasa aka sabon shirinsa mai suna IGIYAR ZATO, wanda yake dab da fara sakinshi ga masu kallo.

“Dokar Nigeria ta bani damar na Shirya fim matukar ba zan sabawa dokokin hukumar tace Fina-Finai ba, don haka masu yi min barazana sai ku yi ta yi, amma sai na saki shirina na IGIYAR ZATO “.

Shugabannin Kananan hukumomi 3 a Kano sun fice daga APC zuwa NNPP

Mustapha Naburaska ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai, ranar asabar a Kano.

Naburska yace dokar kasa ta bada damar duk shugaban da yayi mulki kuma ya gama a matayinsu na masu shirya fina-finai suna da damar shirya fim wanda yayi kama da yadda shugabancinsa yakasance, domin hakan zai taimakawa al’umma su fahimci shugaban yayi abin arziki ko kuma a kasin hakan.

Adam A Zango ya Bayyana Dalilan da Suka sa ya Daina Fitowa a Fina-Finan Kannywood

Ya kara da cewa “la’akari da wannan doka ne yasa na kirkiri wannan shiri na kuma sa masa suna IGIYAR ZATO, domin hakan zai sa al’umma su san yadda gwamnatin data gabata a Kano ta yi abun arziki ko kuwa.

“Ban shirya wannan fim din don yin isgilanci ko cin mutunci gemu ko masu gemu ba, sabanin yadda wasu suke ta fadar cewa Ina kokarin cin mutunci gemu.ko mahaifina fuskarshi cike take da kasunba da gemu dan haka masu wannan tunani su daina bani da shirin cin zarafin masu gemu”. A cewar Naburaska

Nabursaka yace yana yiwa al’umma Albishir da cewa su tanadi buhu-buhun dariya domin akwai abubuwan ban dariya sosai a ciki Shirin.

Al’umma da dama na sukar kokarin shirya shirin da Naburaska yake yi na shirya fim din IGIYAR ZATO saboda yadda yayi shigar masu gemu, don haka suke ganin yana kokarin shirya fim din ne don cin mutunci gemu da masu shi.
.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...