Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya karɓi wasu shugabannin kananan hukumomi guda 3 yan jam’iyyar APC da suka sauya Sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
Gwamnan ya karbe su ne zuwa jam’iyyar NNPP a ranar asabar din nan a gidan gwamnatin jihar Kano.
Rundunar Yan Sandan Kano ta Bayyana Shirin ta Kan Ziyarar Matar Tinubu
1. Nasarawa: Hon. Auwal Lawan Aramposu
2. Garin Malam: Mudassir Aliyu
3. Dawakin Tofa: Hon. Ado Tambai Kwa .
Sai mataimakin shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Hon. Garba Yahaya Labour .
Da yake jawabi gwamna Abba Kabir ya yabawa shugabannin kananan hukumomi bisa yadda suka yi watsi da jam’iyyar APC suka koma jam’iyyar NNPP.
Adam A Zango ya Bayyana Dalilan da Suka sa ya Daina Fitowa a Fina-Finan Kannywood
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a farkon makon nan da muke bankwana da shi shugaban karamar hukumar Nasarawa Auwal Lawan Shu’aibu ya aiyana ficewar sa daga APC zuwa NNPP.
Kwanaki kadan ne dai suka ragewa dukkanin shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano wa’adin mulkinsu ya kare.