Tinubu Ya Bayar da Sabon Umarni ga Yan Nigeria

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya wajabta karanta alkawarin biyayya ga Najeriya ( National Pleged) a duk tarukan gwamnati da na jama’a a kasar.

Kakakin shugaban kasar Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ranar Alhamis inda ya ce yin hakan nuna girmamawa ne ga kasa da kuma karfafa biyayya ga dokokin kasa tare da alkinta al’adu da martaba kasa.

Dawo da Sanusi Matsayin Sarkin Kano Ba Zai Haifawa Kano Da Mai Ido Ba – Wata Kungiya ga Majalisa

Shugaban ya jaddada bukatar yin biyayya ga manufofin kasa da nuna kima ga dokokin kasa.

Da dumi-dumi: Kungiyar Kwadago ta Bayyana Ranar Fara Yajin Aiki a Nigeria

Taken na yi wa Najeriya alkawarin biyayya wanda Tinubu ya ce a yi bayan rera taken kasa, na neman yan kasa su zama masu gaskiya da biyayya ga kasarsu.

Umarnin ya zo ne daidai lokacin da Najeriya ke fama da rikice-rikice da tashin hankali tsakanin arewaci da kudancin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...