Yadda Kotu ta umarci DSS da ta biya Wani direba Naira Miliyan 5

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ci tarar ma’aikatan gwamnatin tarayya Naira Miliyan 5 saboda kamawa tare da tsare wani direban da ke Abuja, Sanusi Shuaib ba bisa ka’ida ba.

Kotun ta kuma umarci hukumar DSS da ta gaggauta sakin direban da ke tsare tun watan Maris din 2023.

Direban da aka tsare ta hannun lauyansa, Bala Dakum, ya maka hukumar DSS a gaban kotu domin kalubalantar tsare shi ba tare ba bisa ka’ida ba tun bayan kama shi.

Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano ta Bayyana Yadda Zata Yaki Yan Kasuwa Masu Boye Kayan Masarufi

Dakum ya yi zargin cewa bayan kama wanda yake karewa, hukumar DSS ta zarge shi da mallakar makamai da ake zargi da aikata ta’addanci kuma yana hannun DSS tun a lokacin.

Sai dai lauyan ya roki kotun ta sake shi, ta kuma biya shi diyyar Naira miliyan 50 na tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Ba zamu lamunci yadda ake yada dokokin karya na Hukumar mu ba – KAROTA

Da yake yanke hukunci a kan lamarin a ranar Alhamis, Mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya ce hukumar ta DSS ta yi fatali da sashe na 35 na kundin tsarin mulkin kasar nan da ya haramta tsare duk wani dan Najeriya sama da tsawon sa’o’i 48 ba tare da umarnin kotu ba.

Olajuwon ya ce hukumar ta DSS a ranar 29 ga Maris, 2023, ta samu umarni daga babbar kotun tarayya da ta tsare direban na tsawon kwanaki 20 kacal don bincikar shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu idan an tuhume shi da aikata wani laifi.

Olajuwon ya ce duk wanda aka tsare har cikin kwanaki 20 to anyi hakan ba bisa ka’ida ba,

Ta yi nuni da cewa hukumar DSS ta tauye hakkin direban na yin tafiye-tafiye domin gudanar da harkokin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...