Daga Umar Ibrahim Kyarana
Wata gobara da ta tashi inda ta lalata kayayyakin abinci da Dabbobi da kayan sawa na dubban Nairori a garin Torankawa da ke karamar hukumar Bunkure.
Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da aka karantawa mai martaba Sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa a yau Laraba 07/02/2024 a fadar sa.
A cewar rahoton daga Galadiman Rano Hakimin Bunkure Alhaji Muhammad Isa Umar, ya bayyana cewa gidaje bakwai masu dakuna ashirin da takwas sun kone kurmus yayin gobarar.
Rahoton da aka karanta ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, kuma gobarar ta tashi ne daga wani wurin dafa abinci na gidan Ya’u Haladu wanda ta kai ga sauran gidajen dake makwabta da inda gobarar ta tashi.
Da yake karbar rahoton, Sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa ya girgiza matuka game da jin lamarin, kuma ya bukaci mutane musamman mata da su tabbatar da kashe wuta bayan su ne gama amfani da ita saboda gudun afkuwar hakan a nan gaba.
Ƙaranci Sadaki: Mal Ibrahim Khalil ya kalubalanci Batun Naira 100, ya fadi hakikaninsa
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran shiyyar Rano Nasiru Habu Faragai ya aikowa kadaura24.
Sarkin, ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya mayar wa wadanda suka yi asarar abubuwan da suka rasa, ya kuma yi addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar irin wannan hadari.
Da aka yi hira da shi jim kadan da zama a fadar, Hakimin kauyen Torankawa Alhaji Ali Ado ya yi karin haske kan yadda lamarin ya kasance.
A wani labarin kuma a yau ne Sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa ya karbi bakuncin sabon kwamandan hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa mai kula da yankin Rano. Alhaji Ibrahim Baba Yaro wanda ya ziyarci Sarkin a fadarsa domin gabatar da kansa tare da neman albarkar Sarkin.
Sarkin, ya yi maraba da sabon Kwamandan yankin, tare da yi masa fatan yin koyi da abokin aikin sa da ya bar yankin ta hanyar zaman lafiya da mutanen yankin domin samun nasarar aikinsu.