Mun Dukufa Neman Hanyoyin Magance Tsadar Kayan Abinchi a Nigeria – Tinubu

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Ministan Kudi da cigaban Tattalin Arziki, Mista Olawale Edun, a jiya, ya ce gwamnatin tarayya ta damu sosai da tashin farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi a Nigeria.

Yace halin da ake ciki ya tilastawa gwamnatin tarayya neman hanyoyin da zata bi domin magance mawuyacin halin da al’ummar Nigeria suke ciki.

Da dumi-dumi: Shugaban Karamar Hukuma a Kano Ya Ajiye Aikinsa

Ministan ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin wata ganawar da ya yi da tawagar kasar Jamus da ta kai ziyara, karkashin jagorancin ministar tattalin arzikin kasar, Ms Svenja Shulze.

Kalaman na Edun ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar jihar Neja suka gudanar da zanga-zanga a jiya, yayin da wasu matasa da mata suka nuna bacin ransu game da tsadar kayan Abinchi da Ake fuskanta, sakamakon fitar da kayan Abinchi zuwa Kasashen Waje da wasu yan Kasuwa ke yi.

Iftila’i: Gobara ta Hallaka Wani Yaro Dan Shekara 4 a Kano

Da yake magana tare da Ministan Edun ya ce, “Ina ganin batun tashin farashin ya shafi gwamnati da kowa da kowa a Najeriya,” kuma an dauki wasu manyan matakai don magance mawuyacin halin da ake ciki.

“Shugaban kasa ya sa baki a wannan fanni don samar da hatsi, takin zamani ga manoma da kuma kawo karin gonaki – shinkafa, alkama, masara, rogo – don kara yawan amfanin gona wanda hakan zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki.

“Kuma, ba shakka, muna tsakiyar noman rani, kuma muna sa ran samun amfanin noman rani mai kyau wanda zai sanya farashi kayan Abinchi ya sakko.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...