Da dumi-dumi: Shugaban Karamar Hukuma a Kano Ya Ajiye Aikinsa

Date:

Daga Khadija Sanusi Gwadabe

 

Shugaban Karamar hukumar ungoggo Engr. Abdullahi Garba Ramat ya ajiye aikin sa Inda ya mika ragamar tafiyar da karamar hukumar ga Mataimakinsa.

Ramat ya shugabanci karamar hukumar ungoggo tun daga shekara ta 2021 zuwa jiya litinin da ya ajiye aikin.

Tsadar Abinchi: Abubuwa 3 da Gwamnan Kano Ya Fadawa Yan Kasuwa Yayin Ganawar sa Da Su

“Alhamdullah, a yau na Mika ragamar tafiyar da karamar hukumar ungoggo ga mataimakina . Na yi iya kokarina na, ta hanyar samar da daruruwan aiyukan raya kasa, na kuma sami lambobin yabo da dama daga ciki har da Gwarzon shugaban karamar hukumar wanda majalisar dokokin jihar kano ta bani. Mu Mun Matsa…💪🏻” Ramat ya rubuta a shafinsa na Facebook

Ali Nuhu Ya Ziyarci Sarkin Kano, A Karon Farko

Ramat wanda ya ajiye aikin nasa cikin wani dan kwarya-kwaryar biki, inda ya bada jari ga mata 500 jari tare kuma da kaddamar da Hatimin karamar hukumar, wanda za a rika amfani da shi a duk wani abu da ya shafi mulkin karamar hukumar.

Tsohon shugaban karamar hukumar ya ajiye aikin ne kwanaki Kadan kafin karewar wa’adin mulkinsu na tsahon Shekaru 3.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...