Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta kama daya daga cikin wadanda ake zargi da farwa Jami’anta.
Hukumar ta sami nasarar kama matashin mai suna Saifullahi Haruna jim kadan bayan da wasu ɓata gari suka farwa Jami’an Hukumar wadanda suke bincike ababen hawa a kan titin Panshekara cikin burnin Kano.
Wasu ɓata garin matasa ne suka farwa Jami’an na KAROTA da misalin karfe 3 na dare a kan titin Panshekara cikin burnin Kano. Hukumar ta ce ba za ta zuba ido ta kyale ana cin zarafin Jami’anta ba, domin kuwa aiki suke bisa tsarin doka.
Kadaura24 ta rawaito Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da Jama’a na hukumar Nabulusi Abubakar ya sanyawa hannu.
Tuni dai Hukumar ta miķa wanda ta kama wajen Baturen Yansandan yankin da abin ya faru, domin fadada bincike tare da daukar matakin kama ragowar domin gurfanar da su gaban Shari’a.
Rundunar Yan sandan Kano Ta Kama Wani Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane
Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ya ce ya zama wajibi Hukumar ta mika godiyarta ga al’umma musamman waðanda suke ankarar da ita wani gyara idan buķatar hakan ta taso
Ya ce ķofar Hukumar a buðe take ga duk wanda yaga wani gyara ko shawara ya sanar da Helkwatar Hukumar ta KAROTA ko ya same mu a kan Lambar Waya 08023608861 domin ciyar da aikin Hukumar da jihar Kano ta ɓangaren Sufuri gaba.