‘Yan Sandan Kano Sun Kama Wasu ‘Yan Daba da akai hayarsu Don Tada Tarzoma a Wajen Zabe

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke wasu ‘yan daba da ake zargin an dauko hayar su domin kawo cikas a zaben da aka gudanar a karamar hukumar Kunchi a jihar.

Usaini Gumel, kwamishinan ‘yan sandan jihar ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar.

Yanzu-yanzu INEC ta Bayyana Dalilan ta na Dkatar da Zaɓen Kunchin da tsanyawa

Gumel wanda bai bayyana adadin mutanen da aka kama ba ya ce yan dabar an kama su ne dauke da da aka makamai.

Ya ce wadanda ake zargin wani dan siyasa ne da ke takara a zaben ya dauki hayar su.

“Mun ga wata babbar mota dauke da mutane gefen hanya. Da farko mun zaci man fetur din motar ne ya kare. Amma muka je kusa dasu sai muka gansu da makamai.

Zaben Cike Gurbi: INEC ta Magantu Kan Sace Akwatunan Zabe a Kano

“Wani Abdulrazaq Muhammad wanda aka fi sani da Mai Salati daga karamar hukumar birnin Kano ya shaida mana cewa wani mutum da ya ke takara a yankin ya gayyace su.

“Za mu tuntubi mutumin domin tabbatar da cewa ko yana cikin yan takarar da kuma dalilin da ya sa ya gayyace su yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...