Hukumar Zakka ta jihar Kano ta raba Zakkar Naira Miliyan Goma ga mutane Dubu a Kano

Date:

Daga Surayya Abdullahi Tukuntawa

Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano ta kaddamar da raba Zakkar Wannan Shekara ga Mabukata Dubu Daya a jihar nan.

Shugaban Hukumar Malam Usman Yusuf Makwarari ne ya bayyana hakan yayin da yake gabata da jawabinsa a wajen taron raba Zakkar.

Sheikh Usman Makwarari yace dama aikin Hukumar shi ne karbar Zakka daga wajen Mawadata Sannan su mikata ga Mabukatan jihar Kano.

Yace kwamitin karbar Zakka daga mawadata da kamfanoni da Hukumar ta kafa ya samu gagarumar nasarar karbo Zakka da sadaka daga mawadatan dake jihar Kano.

A Jawabinsa Babban Daraktan Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano Alhaji Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa yace Wannan Naira Miliyan Goma da Suka raba a yau somin tabi ne, nan gaba zasu Kara zabo Mabukata a jihar nan domin basu zakkar da aka tara.

Yace Mawadata a Kano sun yi abin Daya dace wajen baiwa Hukumar Zakkar da Kuma sadaka domin rabawa Masu karamin karfi don kakkabe talauci a Cikin al’umma Kamar yadda yake a addinin Musulunci.

Safiyanu Gwagwarwa yace an rabawa Mutane Dubu daya Naira Dubu Goma kowanne su, Wanda hakan ya Kama Naira Miliyan Goma.

Ya bukaci wadanda suka karbi Zakkar dasu yi amfani da ita ta hanyar data dace , domin cimma Manufar data sa akace a bada zakka a addinin Musulunci.

Kadaura24 ta rawaito Wasu daga Cikin wadanda suka karbi Zakkar sun baiyana godiyarsu ga Hukumar da kuma gwamnatin jihar Kano,tare da bada tabbacin yin amfani da kudin ta hanyar data dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...