Hukumar Zakka ta jihar Kano ta raba Zakkar Naira Miliyan Goma ga mutane Dubu a Kano

Date:

Daga Surayya Abdullahi Tukuntawa

Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano ta kaddamar da raba Zakkar Wannan Shekara ga Mabukata Dubu Daya a jihar nan.

Shugaban Hukumar Malam Usman Yusuf Makwarari ne ya bayyana hakan yayin da yake gabata da jawabinsa a wajen taron raba Zakkar.

Sheikh Usman Makwarari yace dama aikin Hukumar shi ne karbar Zakka daga wajen Mawadata Sannan su mikata ga Mabukatan jihar Kano.

Yace kwamitin karbar Zakka daga mawadata da kamfanoni da Hukumar ta kafa ya samu gagarumar nasarar karbo Zakka da sadaka daga mawadatan dake jihar Kano.

A Jawabinsa Babban Daraktan Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano Alhaji Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa yace Wannan Naira Miliyan Goma da Suka raba a yau somin tabi ne, nan gaba zasu Kara zabo Mabukata a jihar nan domin basu zakkar da aka tara.

Yace Mawadata a Kano sun yi abin Daya dace wajen baiwa Hukumar Zakkar da Kuma sadaka domin rabawa Masu karamin karfi don kakkabe talauci a Cikin al’umma Kamar yadda yake a addinin Musulunci.

Safiyanu Gwagwarwa yace an rabawa Mutane Dubu daya Naira Dubu Goma kowanne su, Wanda hakan ya Kama Naira Miliyan Goma.

Ya bukaci wadanda suka karbi Zakkar dasu yi amfani da ita ta hanyar data dace , domin cimma Manufar data sa akace a bada zakka a addinin Musulunci.

Kadaura24 ta rawaito Wasu daga Cikin wadanda suka karbi Zakkar sun baiyana godiyarsu ga Hukumar da kuma gwamnatin jihar Kano,tare da bada tabbacin yin amfani da kudin ta hanyar data dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...