Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kotun koli ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke na soke nasarar Gwamna Kabir Yusuf na jihar Kano.
A ranar Juma’a ne wasu alkalai guda biyar suka tabbatar da cewa, kotun daukaka karar ta yi rashin fahimta kan soke kuri’u 165,616 na Gwamna Abba Kabir Yusuf .
Da dumi-dumi: Kotun Ƙoli ta Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnan jihar Bauchi
Alkalin kotun mai shari’a Inyang Okoro ya kuma bayyana cewa batun kasancewar Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar ba, wani lamari ne da ya kamata ayi shi gabanin zabe.
Wannan kotu ta ci gaba da tabbatar da cewa batun tsayar da dan takara ko daukar nauyin zabe kwata-kwata hakki ne na jam’iyya ,” inji shi.