Kwamishinan Yan Sanda a Kano ya yaba da Gudummawar yan Kanywood a bangaren tsaro

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

Rundunar Yan Sanda ta Kasa reshen jihar Kano tasha alwashin cigaba da bada Gudunmawar ta ga Masana’atar Shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Saboda da irin Gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta harkokin Tsaro a jihar Kano.

Kwamishinan Yan Sanda reshen jihar Kano CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana hakan Yayin daya karbi bakuncin Kungiyar Matan Kanywood da Kuma tawagar mashiryin rishirin fin din A Duniya Taijjani Asase Kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na Rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya Sanar Cikin Wata sanarwa da ya fitar.

Kwamishinan yace Yan wasan Hausan Suna bada tasu Gudunmawar wajen inganta tsaro ta Hanyar wayar da Kan al’umma da Kuma ilimantar da su Dangane da harkokin tsaro.

“Sha’anin tsaro Abu ne Daya Shafi kowa don haka muke Bukatar ku cigaba da bada kyakykyawar Gudunmawar da kuke bayarwa don inganta tsaro, Ina baku tabbacin Rundunar mu zata cigaba da Mara Muku baya a aiyukan da kuke na fadakar da al’umma.”Inji CP Sama’ila Dikko

Da yake nasa Jawabin Shugaban Kamfanin dake Shirya fun din a Duniya Taijjani Asase yace sun je ofishin Kwamishinan domin bashi tabbacin zasu cigaba da bada Gudunmawa a fina-finan su wajen nuna darajar Yan Sanda.

Ya ce zasu cigaba da nuna kyakykyawan halayen Yan Sanda da Kuma nuna Hanyoyin da za’a Magance Matsalar tsaro a unguwanni da Sauran garuru.

Tijjaniya Asase yace zasu gyara duk kura-kuran da suke yi a fina-finansu a sha’anin da ya Shafi tsaro da aiyukan Yan Sanda.

17 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Daga Isa Ahmad Getso ‎ ‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana...

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

  Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin...

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   A karon farko an hadu tsakanin...

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...