Tinubu ya rage yawan masu yi masa rakiya yayin tafiye-tafiyensa

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar rage yawan jami’an da za su riƙa yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je a ciki da wajen Nigeria.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai ranar talata.

Talla

Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami’an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa.

INEC ta Sanya Ranar da Zata Gudanar da Zabukan Cike Gurbi a Kano

Sanarwar ta bayyana cewa matakin, wani yunƙuri ne na rage yawan kuɗaɗen da jami’an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.

Ta ce yawan jami’an da za su riƙa yi wa shugaban ƙasa rakiya zuwa ƙasashen waje, nan gaba ba za su wuce jami’ai 20 ba. Haka zalika, Ngelale ya ce Tinubu ya ba da umarnin a daina tura ɗumbin jami’an tsaro zuwa wata jiha a duk lokacin da zai kai ziyara can, maimakon haka za a riƙa amfani da jami’an tsaron da ke jihar ne kawai don tabbatar da tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...