Kudaden Kananan Hukumomi: Kotu Ta Bai Wa Gwamnatin Kano Wa’adi

Date:

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba wa gwamnatin Kano wa’adin kwanaki bakwai ta kawon dalilin da zai hana ta amsa bukatar shugabannin kananan hukumomin jihar 44 na hana gwamnatin amfani kudadensu.

Jaridar Aminiya ta rawaito mai Shari’a Donatus Okorowo ne ya bayar da wannan umarni a makon jiya, bayan lauyoyin bangaorin sun gabatar da hujjojinsu a game da bukatar masu karar.

Sai dai Mai shari’a Okorowo ya ki amincewa da bukatar kananan hukumomin ta hana Gwamna Abba Kabir Yusuf amfani da kudaden nasu.

Talla

Rikicin kudadaen kananan hukumomin ya kunno kai ne bayan majalisar zararwar jihar ta amince a biya kashi 70 na kudin aikin gina gadar sama a Kofar Dan-Agundi daga asusun kananan hukumomin jihar, a yayin daga gwamnayin jihar za ta biya ragowar kashi 30.

A zaman farkon na ranar 28 ga Disamba, 2023, alkalin ya umarci wadanda ake kara su bayyana a gabansa a ranar 3 ga watan Janairu su kawo dalilin da zai hana shi amsa bukatar masu kara.

 

Sannan ya amince da rokon da suka gabatar na mika takardar sammaci ga wadanda ake kara ta hannun wakilansu.

Dan Jaridar Da Ya Tona Asirin Digirin Dan Kwatano Ya Koka

Dalilin Zuwa Kotu

Kungiyar Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) reshen kananan hukumomi 44 na Jihar Kano ne suka maka gwamnatin jihar a kotun ranar 27 ga watan Disamba, 2023.

Wadanda ake karar su ne gwamnatin jihar, babban lauyanta kuma kwamishinan shari’a da kuma Akanta-Janar na jihar.

Zaman ranar Laraba
A zaman kotun na ranar Labara, lauyan masu kara, Ibrahim Nasarawa, ya shaida wa alkali cewa da farko an dage shari’ar ne domin wadanda ake kara su kawo hujjar da za ta hana kotu amsa rokon masu karar.

Nasarawa ya ce an ba wa wadanda ake kara takardar shari’ar bisa umarnin kotu, amma sun kasa gabatar da hujjojinsu a kwanaki ukun da kotun ta kayyade.

Don haka ya roki kotun da ta amince da bukatar masu kara kamar yadda doka ta 26, dokar kotu ta tanada.

Dangote ya faɗo daga matsayin attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka

Sai dai lauyan gwamnatin jihar, Hafeez Matanmi, ya kalubalance shi da cewa har yanzu bai ga jawaban da masu kara suka gabatar kan lamarin ba, don haka babu yadda zai iya bayar da kariya a kai.

Lauyan wanda ake kara na 3, Okechukwu Edeze, ya ce an yi masa bayanin lamarin ne kasa da sa’o’i 24 kafin zaman kotun na ranar, don haka ya nemi a dage sauraron karar.

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Okorowo ya bayyana cewa, duk da cewa an mika wa wadanda ake kara sammaci yadda ya kamata a ranar 29 ga watan Disamba, 2023, amma ya amince da bayanin lauyansu cewa cewa wa’adin kwanaki uku da aka ba su su amsa ya shiga ranakun hutu

A saboda haka mai shari’a Okorowo ya baiwa wadanda ake tuhuma wa’adin kwanaki bakwai su kawo dalilasnu, sannan ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 11 ga watan nan na Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...