Kotu a Kano ta Umarci a Kamo Mata Wani Jami’in Kwastam

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

 

Babbar kotun shari’ar musulunci dake zaman ta a sabon gari a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’ah, Hamza Garba Malafa ta yi umarnin a kamo mata wani jami’in costom, mai suna Yusuf Isma’il Muktar Mai biscuits. Biyo bayan kin bayyana a kotun a yau Alhamis.

Tun da fari dai wani maraya ne mai suna Abdullahi Shehu Aliyu wanda aka fi sani da baballe, ya yi karar sa kan cewa yana kokarin kwace masa wani katon kango, dake Kawaji layout a Karamar hukumar Nasarawa.

Talla

Rahotanni sun bayyana cewa kimar kango ta kai Naira miliyan hamsin. Wanda ya siya a wajan yayan Yusuf din mai suna Mustapha Isma’il Mai biscuits. Watanni uku da suka gabata.

Dan Jaridar Da Ya Tona Asirin Digirin Dan Kwatano Ya Koka

Kan haka ne lauyan Mai kara Saleh Idris Bello ya yi roko a kamo shi, tin da dai an bashi sammaci amma bai je kotun ba.

Tuni dai alƙalin kotun mai shari’a Hamza Garba ta amince da rokon lauyan masu kara, Inda yace a kamo Yusuf Isma’el Nan da ranar 8/01/23.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...